Mutum Ɗaya Ya Rasu, Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina Ya Jikkata A Hatsarin Mota
Wani mutum ya rasu yayin da wasu suka jikkata a hatsarin mota a Katsina. Hatsarin ya rutsa da wakilan APC daga Sabuwa kan hanyarsu ta zuwa taron yankin Arewa maso Yamma na jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa marigayin mai suna Dalhat Machika na cikin waɗanda suka mutu. Haka kuma tsohon mataimakin gwamna, Sirajo Umar Damari,…