Harin Kwanton Ɓauna: Lakurawa Sun Kashe Sojoji 9, Ɗansanda 1 A Kebbi

[ad_1]

‘Yan ta’addan Lakurawa sun kai harin kwanton bauna kan wata motar sintiri dauke da jami’an soja da ‘yan sandan MOPOL a kauyen Giron Masa da ke karamar hukumar Shanga a Jihar Kebbi, inda suka kashe sojoji tara da dansanda guda, tare da kona motar sintirin.
Majiyarmu ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata yayin da tawagar hadin gwiwa ke sintiri domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.
  • Ƙungiyar Matasan Jihar Filato Ta Yi Zanga-Zanga Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro
  • Neymar Ya Fi Messi, Ronaldo Da Mbappe Hazaka A Kwallon Kafa – Cafu
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, bayan samun rahoton lamarin, ya garzaya zuwa Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda aka ajiye gawarwakin sojojin tara da dan sandan daya a dakin ajiyar gawa.
Haka kuma ya ziyarci sashen da ake kula da marasa lafiya inda wasu jami’an tsaro biyu ke karbar magani sakamakon raunukan harbin bindiga da suka samu.
Sai dai gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuka kuma mai radadi, yana mai cewa babbar asara ce ba ga hukumomin tsaro kadai ba, har ma ga daukacin al’ummar Jihar Kebbi da kasa baki daya.
Daga asibitin, Gwamna Idris ya wuce Giron Masa inda lamarin ya faru, inda ya duba motar da ‘yan bindigar suka kona.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa zai garzaya Abuja domin ganawa da Babban Hafsan Sojojin Kasa, domin mika sakon ta’aziyyar gwamnati da al’ummar Jihar Kebbi kan wannan babban rashi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *