Shugaba Tinubu Ya Amince Da Biyan Naira Tiriliyan 3.3 Domin Warware Bashin Wutar Lantarki

[ad_1]

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani shirin biyan kuɗi har Naira tiriliyan 3.3 domin warware tsofaffin basussukan da suka addabi ɓangaren wutar lantarki, a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen farfaɗo da tsarin samar da wuta da kuma inganta ayyukansa gaba ɗaya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan cikakken nazari kan basussukan da suka taru tsawon sama da shekaru goma, daga watan Fabrairu na 2015 zuwa Maris 2025, inda aka tabbatar da cewa adadin Naira tiriliyan 3.3 shi ne cikakken kuɗin da za a biya domin rufe wannan lamari gaba ɗaya.

  • 2027: Gwamna Ododo Ya Shirya Gangamin Goyon Bayan Tinubu A Kogi
  • 2027: Tinubu Na Son A Naɗa Shi Sarauta Ne, Ba Zaɓe Ba — Dino Melaye

Ya ƙara da cewa tuni aka fara aiwatar da shirin, inda tashoshin samar da wutar lantarki guda 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar bashin da ya kai Naira tiriliyan 2.3, yayin da gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 501 domin fara biyan kuɗin, ciki har da Naira biliyan 223 da aka riga aka fitar, tare da ci gaba da sauran biyan kuɗaɗen a matakai na gaba.

Masu ruwa da tsaki na ganin cewa wannan mataki zai ƙarfafa dukkan sassan tsarin wutar lantarki, tare da inganta daidaiton samar da wuta da kuma rage yawan tangarɗar da ake samu, wanda hakan zai amfanar da ‘yan ƙasa da masana’antu baki ɗaya.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, ya bayyana cewa shirin ba wai biyan basussuka kawai ba ne, har ma yana da nufin dawo da amincewa a bangaren, ta hanyar tabbatar da cewa masu samar da iskar gas da tashoshin wuta suna samun haƙƙinsu, tare da inganta tsarin mitoci da farashin sabis domin ya dace da ingancin wutar da ake samu.

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da masu ruwa da tsaki suka bayar wajen warware wannan matsala, yana mai tabbatar da cewa mataki na gaba na shirin, wato Series II, zai fara a wannan kwata, domin ci gaba da gyaran ɓangaren wutar lantarki da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *