Iyabo Obasanjo ta koma APC, ta ayyana takarar gwamnan Ogun

[ad_1]



Farfesa Iyabo Obasanjo, ’yar tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ta koma jam’iyyar APC tare ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar gwamnan Jihar Ogun a zaɓen 2027.

Ta bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata hira a gidan rediyon Eagle7 FM.

Iyabo, wadda ta taɓa wakiltar Ogun ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2007 zuwa 2011, ta dawo siyasa bayan shekaru 15.

Ta kammala rajistar zama mambar jam’iyyar APC a yankin Ibogun da ke Ƙaramar Hukumar Ifo.

Tsohuwar Sanatan ta ce matsin lamba daga magoya bayanta ne ya sa ta yanke shawarar dawowa siyasa, domin suna ganin ita ce ta fi dacewa ta jagorancin jihar.

Ta ce ba za ta koma jam’iyyar PDP ba saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyar.

Ta kuma yi la’akari da jam’iyyar ADC, amma ta ce har yanzu jam’iyyar ba ta shirya sosai ba.

A cewarta, yawancin mutanen da suka nemi t dawo siyasa a yanzu suna cikin jam’iyyar APC, wanda hakan ya sa ta zaɓi jam’iyyar.

Iyabo ta kuma bayyana cewa ba ta da niyyar komawa Majalisar Dattawa ko karɓar muƙamin kwamishina.

“Takarar gwamna kaɗai na ke son tsayawa” in ji ta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *