An Yi Wa Dabbobi Sama Da Miliyan Biyar Allurar Rigakafi A Kano

[ad_1]

A ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na ƙara haɓaka fannin kiwon dabbobi a Jihar Kano, Hukumar Kula da Bunƙasa Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano, ta yi wa dabbobi sama da miliyan 5.5 allurar rigafin kare su daga kamuwa da cututtuka daban-daban.

A cewar hukumar, ta gudanar da wannan aiki na rigakafin ne a shekaru uku da suka gabata.

Jami’in aikin a jihar, Ibrahim Garba Muhammad ne ya sanar da haka a Kano, wanda ya sanar da cewa; amma tun da farko, hukumar ta tsara za ta yi wa dabbobi miliyan 5.5 ne rigakafin cututtuka daban-daban, inda ya ƙara da cewa; a yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da aikin a faɗin jihar.

  • An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani
  • Barkewar Kwalara: Ya Kamata A Dakatar Da Yin Kunu Da Zobo – Karamin Ministan Muhalli

“Ba na jin akwai wata jiha ɗaya a ƙasar nan da za ta iya bugun ƙirje ta ce, ta yi wa dabbobi har kimanin miliyan biyu allurar rigakafin dabbobi a shekaru uku da suka gabata, amma a Jihar Kano an yi hakan, ciki har da kuma zuba jarin sama da naira biliyan ɗaya, domin bayar da horo ga Fulani Makiyaya, don samar da wadatacciyar Madarar Shanu a jihar,” in ji shi.

Muhammad ya ƙara da cewa, KSADP ta kuma samar da asibitin duba lafiyar dabbobi a yankin Danshosiya da ake kiwon dabbobin a zamanance, inda aka keɓe kimanin hekta sama da 2,000, musamman domin a ƙara samar da wadataccen abincin dabbobin.

Ya ci gaba da cewa,  an kuma gyara kusan kimanin hekta 1,000 a yankuna 20, inda aka miƙa su ga ƴan kasuwa a fannin kiwon, domin gudanar da yin sana’ar kiwon.

A cewar tasa, daga cikin ƙoƙarin da KSADP ke yi na ƙara bunƙasa fannin kiwon dabbbobi, musamman domin samun riba da kuma samar musu da kasuwa, inda ya sanar da cewa; an kuma ƙara sabunta aikin kasuwar sarrafa  Fura da Nono da ke   Ƙofar Wambai a jihar ta Kano.

Ya ci gaba da bayyana cewa, an samar da ɗakin adana Mararar Shanu a kasuwar, wanda za a iya adana Madarar sama da 3,000 da hakan zai taimaka wa masu sana’ar tare da ba su damar amfana yadda ya kamata.

Kazalika ya sanar da cewa, an samar da cibibiyon karɓar Madarar Shanu kimanin 98 tare da kammala su da kuma samar musu da na’urorin adana Madarar Shanu kimanin guda 40.

Jami’n ya ci gaba da cewa, sauran cibiyoyin da suka fara gudanar da aikinsu, za su sanya a iya samar da litar Madarar Shanu miliyan 15 a duk shekara, inda ya ƙara da cewa; cibiyoyin za su kuma taimaka wajen samar da sauƙi ga matan Fulani.

Aikin na bunƙasa fannin kiwon na dabbobi da ake gudanarwa a Jihar Kano, Bankin IsDB ya zuba kuɗi da suka kai kimanin dala miliyan 95, musamman don yin kiwon dabbobin, domin samun riba da kuma samar wa da masu sana’ar kasuwa tare da ba su kyakkyawan horo.

Alfanun da aka samu a ƙaraƙashin aikin, ya kai na kimanin naira biliyan 39.2, wanda kuma KSADP ta samar da kayan aiki na zamani tare da samar da shirin bayar da horo da aka samar a shiyoyi uku na Jihar Kano da suka haɗa da Kadawa, Kano ta tsakiya, Ɗanbatta, North da kuma a Gaya ta kudu, inda aka raba wa manoma Taraktocin noma 98 da kuma yin girbin amfanin gona kimanin guda 48.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *