Gobara A Ƙananan Masana’antu Da Ke Dakata: An Tunatar Da Gwamnan Kano Kan Alƙawarin Miliyan 100 Da Ya Yi
[ad_1]
Yau kusan shekaru ɗaya da tashin gobara a rukunin ƙanana da matsakaitan masana’antu da ke Unguwar Dakata a Jihar Kano, wanda sanadiyar hakan aka samu sallawatar dukiya na miliyoyin naira, kamar yadda shugaban ƙungiyar ƙananan masana’antu, Alhaji Zulkiblu Alasan Umar, ya tabbatar da haka ga manema labarai.
Shugaban ƙungiyar ya ce a ziyarar jaje da gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir ya kawo ga waɗanda abin ya shafa ya yi masu alƙawarin zai tallafa masu da kuɗi har naira miliyan 1OO, amma har ya zuwa aiko da wannan rahoton babu ko ƙwandala da ya shigo.
- Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran
- Dalilin Da Ya Sa Sin Ci Gaba Da Zama Babbar Kasuwar Ciniki Ta Duniya
Shugaban ya tunatar da gwamnan ganin yadda waɗanda abin ya shafa suke ba da gudunmuwa wajen samar da aikin yi ga ƴan asalin jihar da ma wasu al’umma da suka fito daga wajen jihohi baya ga samar da kuɗaden shiga ga gwamnatin jihar da ta tarayya.
Alhaji Zulkiblu ya ce rukunonin kamfanonin na Dakata sun shahara wajen sarafa man gyaɗa da roba, wanda ya koka kan yadda farashin wutan lantarki ta yi yi tsada, amma duk da haka ya ce idan ana samun wutan akai-akai wannan ba wani matsala ba ne.
Daga ƙarshe, ya jinjina wa gwamnan Jihar Kano kan ƙoƙarin da yake yi wajen samar da hasken wutan lantarki mallaki, matuƙar aka kamala wannan aiki, to masana’antun da ba sa aiki za su tashi, sannan kuma al’ummar jihar za su samu aikin yi.
[ad_2]
Source link