Sojoji Sun Kwato Yankuna, Sun Kashe Ƴan Bindiga 65 A Zamfara

[ad_1]

Dakarun Operation FANSAR YAMMA sun samu gagarumar nasara a yaƙi da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, inda suka kashe aƙalla ‘yan bindiga 65 ciki har da ɗan wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, a wani zazzafan farmaki da aka kai ta ƙasa da sama a ƙaramar hukumar Tsafe.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya auku ne a ƙauyen Munhaye da ke bayan Kunchin Kalgo, inda aka kashe Kachalla Iliya Sarki, wanda ke daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar kuma ɗan Ado Allero, tare da wasu manyan jagorori irin su Dogo Sule da Iliya Mai Rasha, waɗanda ake zargi da hannu a hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma.

  • Motoci 3 Masu Amfani Da Gas (CNG) Sun Yi Bindiga A Tashar Mota A Kaduna
  • Gwamna Bago, Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Bindiga Da Masu Ba Su Bayanai

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an fara gumurzu mai tsanani ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, 4 ga Afrilu, 2026, inda ɗaruruwan ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari da babura kusan 300 daga yankunan Yan Wari da sansanin Dankarami Gwaska, amma dakarun sojoji tare da taimakon hare-haren jiragen sama suka daƙile su bayan shafe sama da sa’o’i bakwai ana musayar wuta.

Sai dai duk da wannan nasara, an yi asarar rayukan wasu jami’an ‘yan sa-kai guda bakwai da suka taimaka wa sojojin a fafatawar, yayin da rahotanni ke cewa Ado Allero ya tsere daga yankin zuwa garin Yankuzu, inda ake zargin yana ɓoye, yayin da sojoji ke ci gaba da farautarsa da sauran mabiyansa domin murƙushe su gaba ɗaya.

Masana harkokin tsaro sun bayyana kashe Iliya Sarki a matsayin babbar koma baya ga ‘yan bindiga a yankin, suna mai cewa hakan zai raunana tsarin jagoranci da ayyukan ƙungiyar, sai dai sun yi gargadin cewa hakan na iya haifar da ramuwar gayya, don haka an sanya jami’an tsaro cikin shirin ko-ta-kwana a yankunan da ke cikin haɗari yayin da ake ci gaba da aikin share yankunan daga ragowar ‘yan bindigar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *