‘Yan Ta’adda 11 Sun Miƙa Wuya Yayin Da Sojoji Suka Kashe 8 A Borno

[ad_1]

‘Yan Ta’adda 11 sun mika wuya ga sojojin ‘Operation Hadin Kai’, yayin da sojojin suka kashe wasu takwas tare da kama wasu biyu da ake zargi da samar da kayayyaki ga ‘yan ta’adda a yayin da sojojin suka tsananta kai hare-hare a maɓoyar ‘yan ta’adda a fadin jihar Borno.
Jami’in Yada Labarai na Rundunar Hadin Kai ta Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Bunkasa Sayayya Da Bude Kofa A Shekarar 2026
  • Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Dalilin Sakin Mutane 70 Da Ake Zargi Da Ta’addanci
A cewar Uba, ci gaba da kai hare-hare a karkashin ‘Operation Desert Sanity V’ ya tilasta wa ‘yan ta’adda ajiye makamansu a kan titin Azir-Wajiroko a ranar Asabar, 10 ga Janairu, 2026.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a ranar Juma’a, 9 ga Janairu, sojoji sun gudanar da ayyukan shara a dajin Bula Gaida, inda suka lalata wurare da sansanonin ‘yan ta’adda da dama a Dagumba, Bonne, Yaganari, Gosuri, da Umchile, ciki har da wadanda ke karkashin manyan kwamandojin Abu Nazir da Abu Ahmed.
Hakazalika, hare-haren da a kai hari a Yale da Bula Gaida sun tilasta wa ‘yan ta’adda tserewa, wanda ya haifar da lalata wasu cibiyoyin jigilar kayayyakin ta’addanci da kuma kwato karin makamai, harsasai, da kuma manyan bindigogi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *