Atiku Ya Nuna Damuwarsa Kan Kama ‘Yan Adawa, Ya Nemi A Saki El-Rufai

[ad_1]

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi cewa kama mutane saboda ra’ayinsu na siyasa barazana ce ga dimokuraɗiyya.

Ya faɗi hakan ne kan tsare Abubakar Malami da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

  • An Kashe Ƴan Ta’adda 500 A Hare-haren Ngoshe Da Fatori – Zulum
  • Daƙile Taron Ƙasa Na Abuja: Ɓangaren PDP Ƙarƙashin Turaki Ya Caccaki Ɓangaren Wike

Atiku ya ce irin wannan mataki ya saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Bayan dawowarsa daga Umrah daga ƙasar Saudiyya, ya kai ziyara ga Malami domin nuna goyon bayansa.

Haka kuma ya buƙaci a saki El-Rufai da sauran ‘yan siyasar da ake tsare da su.

Atiku ya jaddada cewa bai kamata a tsare kowa ba saboda yana cikin wata jam’iyya daban ko yana da ra’ayi saɓanin na gwamnati.

Ya ƙara da cewa dimokuraɗiyya tana buƙatar juriya, girmama ra’ayoyi daban-daban da kuma bin doka, yana mai gargaɗin cewa danne masu suka na rage amincewar jama’a da gwamnati.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *