An Gurfanar Da El-Rufai A Kotun Kaduna, An Hana ‘Yan Jarida Shiga
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gurfana a gaban Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar Talata domin fuskantar tuhume-tuhume kan zargin laifukan cin hanci da rashawa.
Ya isa kotun da misalin ƙarfe 9 na safe cikin tsauraran matakan tsaro daga hukumomin yaƙi da rashawa da sauran jami’an tsaro, ciki har da ICPC da DSS, kafin a shigar da shi cikin kotu bayan kusan minti 30.
- Sevilla Ta Raba Gari Da Kocinta Almeyda
- Atiku Ya Nuna Damuwarsa Kan Kama ‘Yan Adawa, Ya Nemi A Saki El-Rufai
An hana ‘yan jarida da suka isa da wajen shiga cikin kotun, lamarin da ya jawo damuwa kan yadda ake tafiyar da shari’ar.
Haka kuma an ƙara tsaurara tsaro a wajen kotun, wanda ya haddasa cunkoson ababen hawa.
Hukumar ICPC ta ce El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da cin hanci da rashawa, ɓatar da kuɗin gwamnati da kuma amfani da muƙami ba daidai ba.
Ana kuma tuhumar wasu mutane tare da shi a wasu shari’o’i daban.
Wannan shari’a na zuwa ne bayan makonni da aka shafe ana tsare da shi, yayin da wasu ke neman a sake shi ko kuma a gurfanar da shi a kotu.
El-Rufai na ci gaba da kasancewa a tsare yayin da shari’ar ke gudana.