HOTUNA: Yadda aka tsaurara matakan tsaro yayin gurfanar da El-Rufai a Kotu

[ad_1]



A wannan Talatar ce Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna bisa zargin aikata laifukan da suka shafi karkatar da kuɗaɗe da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.

Malam El-Rufai ya isa harabar kotun da misalin ƙarfe 9:00 na safe a cikin wata mota ƙirar Hilux fara, tare da jami’an hukumar.

An gan shi tare da jami’an ICPC guda biyu kafin a shigar da shi cikin ɗakin kotu, da taimakon jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya na DSS.

An tsaurara matakan tsaro a faɗin birnin Kaduna kafin gurfanarwar, inda aka jibge jami’an tsaro ɗauke da makamai daga ’yan sanda, DSS, da sauran hukumomin tsaro a wurare masu muhimmanci.

Wakilin Aminiya ya lura cewa jami’an tsaro sun kafa shigayen bincike tare da sanya ido a manyan hanyoyin da ke kaiwa kotun, ciki har da titin Ali Akilu, wanda ya fuskanci cunkoson ababen hawa sakamakon taƙaita zirga-zirga zuwa titi ɗaya kacal.

Haka kuma, an jibge motocin ’yan sanda kusa da Gidan Gwamnati da muhimman mahaɗar hanyoyi, lamarin da ya tilasta wa direbobi da dama, musamman masu nufin zuwa kotu, bin wasu hanyoyi daban.

An taƙaita shiga harabar kotun, inda ’yan jarida da jami’an kotu da aka tantance kaɗai aka bari su shiga, duk da cewa ba a ba su damar shiga cikin ɗakin kotun domin bibiyar shari’ar ba.

Wasu daga cikin abokan hulɗa da magoya bayan tsohon gwamnan sun halarci kotun, ciki har da ’yan uwansa.

Ɗansa, Bello El-Rufai, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa, shi ma ya halarta.

Haka kuma, akwai tsofaffin kwamishinoni da suka yi aiki a gwamnatin El-Rufai, ciki har da Bashir Saidu, Hafsat Baba da Jafaru Sani da suka halarci zaman.

Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna, Hazo, da Sanata Babba Kaita na daga cikin sauran ’yan siyasa da suka halarta.

ICPC ta bayyana a cikin wata sanarwa da kakakinta, Demola Bakare, ya fitar a ranar Litinin cewa za a gurfanar da El-Rufai tare da wani Joel Adoga a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.

Shari’ar mai lamba FHC/KD/73/2026 na ƙunshe da zarge-zargen karkatar da kadarorin gwamnati da mallakarsu ba bisa ƙa’ida ba, da kuma halasta kuɗaɗen haramun.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an shigar da wata ƙara ta daban a kan El-Rufai tare da wani Amadu Sule a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.

A cewar ICPC, ƙarar ta jihar na ɗauke da zarge-zargen amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba, damfara, yunƙurin aikata damfara, da bayar da wata riba ba bisa ƙa’ida ba.

An shigar da tuhume-tuhumen ne a ranar 18 ga Maris, 2026. Duk da cewa an tsara gurfanarwar a Kotun Tarayya a ranar Talata, hukumar ta ce za a sanar da ranar shari’ar kotun jihar daga baya.

Hukumar ICPCn ta ƙara da cewa an riga an miƙa wa tsohon gwamnan takardun sammaci dangane da tuhumar yadda ya kamata, tare da jaddada ƙudurinta na bin doka da oda da kuma tabbatar da gaskiya a shari’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *