Kama El-Rufai Tsagwaron Siyasa Ce Kuma Babu Adalci — Obi

[ad_1]

Peter Obi ya ce kama da kuma gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ba komai ba ne face siyasa.

Da yake magana a Kaduna, Obi ya ce El-Rufai ya dawo Nijeriya da kansa daga Masar, amma ana mu’amala da shi kamar wanda ke ƙoƙarin tserewa.

  • An Gurfanar Da El-Rufai A Kotun Kaduna, An Hana ‘Yan Jarida Shiga
  • Sojoji Sun Kama Mai Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai A Adamawa

Ya jaddada cewa kowa na da haƙƙin a yi masa adalci har sai an tabbatar da laifinsa.

Obi ya kuma buƙaci hukumomi su bar doka ta yi aikinta yadda ya kamata ba tare da son zuciya ba.

Shi da El-Rufai sun shiga jam’iyyar ADC kwanan nan domin ƙoƙarin ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027.

Daga baya El-Rufai ya miƙa kansa ga EFCC, kuma yanzu yana hannun ICPC.

Ya kuma gurfana a kotu yayin da shari’ar ke ci gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *