Sallah: Sibil Difens ta jibge jami’anta 700 don tabbatar da tsaro a Gombe
[ad_1]
Hukumar Sibil Difens a Jihar Gombe, ta sanar da tura jami’anta guda 700 zuwa sassan jihar daban-daban, domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan salla ƙarama.
Wannan matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Buhari Sa’ad, ya fitar a madadin kwamandan jihar, Jibrin Idris.
Rundunar ta bayyana cewa an tsara aikin ne na musamman tsakanin ranakun 19 zuwa 21 ga watan Maris, 2026.
Kwamandan ya bayyana cewa an riga an jibge jami’an a wuraren da ake ganin sun fi buƙatar kulawa, ciki har da filin Idi da hanyoyin da za a bi domin yin hawan salla.
Ragowar wuraren sun haɗa da wuraren shaƙatawa, kasuwanni, tashoshin mota da manyan hanyoyin shige da fice na jihar.
Baya ga kare rayukan jama’a, Jibrin Idris, ya jaddada cewa rundunar za ta sanya idanu kan kadarorin gwamnati da na jama’a domin daƙile masu son yin amfani da lokacin wajen yin ɓarna.
Ya kuma tabbatar da cewa suna aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda.
Yayin da yake jan kunnen jami’an da aka tura su gudanar da aiki da gaskiya da ƙwarewa, kwamandan ya kuma taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Ya ƙarƙare da yin kira ga mazauna jihar da su gudanar da bukukuwan cikin lumana, sannan su kasance masu sanya idanu tare da kai rahoton duk wani ga jami’an tsaro mafi kusa da su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link