Adadin Wutar Lantarki Da Xinjiang Ta Samar Ga Sauran Wurare Daga Makamashi Mai Tsafta Ya Wuce Biliyan 304 Kwh
[ad_1]
Rahotanni na cewa ya zuwa yau Laraba, adadin wutar lantarki da jihar Xinjiang ta aikawa sauran wurare a nan kasar Sin, bisa makamashi mai tsafta ya kai biliyan 304.36 kilowatt-hour, adadin da ya kai kusan kashi 30 cikin 100 na dukkan wutar lantarki da ta samarwa sauran wuraren kasar.
Xinjiang, muhimmiyar tasha ce ta samarwa sauran wuraren kasar Sin wutar lantarki, a cikin tsarin jigilar wutar lantarki daga yamma zuwa gabas, da tsarin samarwa sauran wuraren wutar lantarki bisa makamashi mai tsabta.
Ya zuwa karshen shekara ta 2025, Xinjiang ta gina manyan tasoshin samar da wutar lantarki bisa makamashi mai tsabta 6, masu karfin kilowatts miliyan 10, kuma karfin samar da wutar lantarki daga makamashi mai tsafta ya kai kilowatts miliyan 169, adadin da ya kai kashi 64 cikin 100 na jimillar karfin samar da wutar lantarki a Xinjiang. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link