Eid-fitr: Gwamnatin Kano Ta Sanya Tsauraran Matakai Kan Hawan Sallah Saboda Tsaro

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da tsauraran matakai kan bukukuwan Hawan Sallah mai zuwa, sakamakon sahihan rahotannin sirri da Majalisar tsaro ta jihar ta samu da ke nuna yiwuwar tayar da tarzoma.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa labarai, Ibrahim Wayya ya fitar ta bayyana cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ne zai jagoranci Hawan Idi daga Kofar Mata zuwa Kofar Fatalwa, inda da Hawan Nassarawa kuma za a yi shi a salo na musamman ba tare da hawa dowakai ba.

  • Mataimakin Gwamnan Kano Na Iya Yin Murabus Saboda Barazanar Tsige Shi
  • Trump Ya Ce Amurka Za Ta Ci Gaba Da Yaƙi Da Iran Ba Tare da Taimakon Kowa Ba

Sanarwar ta ƙara da cewa, an dakatar da Hawan Daushe da Hawan Fanisau da kuma Hawan Dorayi, na ɗan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnatin ta ce duk da ƙudurin ta na kare al’adun Kano, za ta fifita kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da doka da oda.

An umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin waɗannan matakai, tare da kira ga jama’a da su kasance masu natsuwa da bin doka tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a lokacin bukukuwan Sallar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *