Ana tursasa wa magoya bayanmu komawa APC a Kano – Kwankwaso
[ad_1]
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce magoya bayansa a cikin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na fuskantar matsin lamba kan shirin gwamnan na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
A kan haka, jagoran na jam’iyyar NNPP, ya bukace su da su rattaba hannun domin rage tashin hankalin da suka tsincin kan nasu a ciki.
Kwankwaso ya yi wadannan makalaman ne a ranar Talata cikin wani sakon bidiyo da mai taimaka masa na kafafen sada zumunta, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ana ganin yunkurin Gwamna Abba na shiga APC ya jawo matsala a dangantakarsa da Kwankwaso, wanda ake wa kallon ubangidansa a siyasa.
Duk da cewa Kwankwaso ya ƙi kiran da ake yi masa na ya bi gwamnan zuwa APC, ya nuna damuwa kan rahotannin cewa ana tilasta wa zababbun shugabanni, ciki har da shugabannin kananan hukumomi, kansiloli, sakatarori, da sauran masu rike da mukamai, su sa hannu a takardu da ke bayyana bangaren siyasar da suke goyon baya.
Ya ce: “Yau, 13 ga watan Janairu 2026, na iso jiharmu mai albarka ta Kano, inda na tarar da abubuwa masu kyau da dama, amma kuma akwai wasu abubuwa marasa dadi, musamman batun tilasta shugabannin kananan hukumomi, kansiloli, sakatarori, da sauran masu mukamai su rubuta bangaren da suke goyon baya, Kwankwasiyya ko Gandujiyya. Wannan abin takaici ne, kuma babu wani masoyinmu da zai ji daɗi da shi,” in ji shi.
Ƙoƙarin samun martanin gwamnati kan wannan zargi bai yi nasara ba jiya. Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Waiya, bai amsa kiran waya ba, haka kuma ba a sami mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.
Kwankwaso ya tuna yadda kungiyarsa ta Kwankwasiyya ta yi haƙuri har zuwa 2023 kafin ta dawo kan mulki a jihar.
Ya ce: “Mun yi haƙuri muka jira 2023, lokacin da jama’a suka fito suka jajirce suka zaɓi wannan gwamnati ta yanzu a jihar, da fatan samun rayuwa mai kyau, damar ilimi, ayyukan yi, da ayyukan raya kasa,” in ji shi.
Kwankwaso ya bayyana siyasar Kano a matsayin fafatawa tsakanin “haske da duhu,” yana mai jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya tana da tsari bayyananne da ba za a iya lalata shi ba.
Ya ce: “Tafiyarmu, duk wanda ya shiga cikinta, sai ka bi tsarin ta. Amma idan ya kauce, sai dai ya sauya sheka. A Kano, muna da zaɓi biyu kawai: haske da duhu. Muna farin cikin cewa jama’a sun fahimci hakan sosai, kuma muna godiya gare su,” in ji shi.
Game da shirin sauya sheƙar gwamnan, Kwankwaso ya ce rikicin ya jawo damuwa ga zababbun jami’an gwamnati a jihar.
Ya ce: “Tun da rikicin sauya sheƙa zuwa wajen Ganduje da Tinubu ya fara, mutane suka shiga damuwa da takaici. Shugabannin kananan hukumomi da dama sun kira ni ta waya; haka kuma wasu kansiloli da ke da damar yin magana da ni, sauran masu mukamai, da ’yan majalisar jihar da dama sun sanar da ni halin da suka tsinci kansu, inda wasu bas a iya barci, wasu ma har karin ruwa,” in ji shi.
Kwankwaso ya ce ya yi shawara da manyan masu ruwa da tsaki, ya yanke hukuncin ba wa dukkan jami’an da ke cikin matsin lamba, ciki har da shugabannin kananan hukumomi, kansiloli zababbu da masu gafaka, da sauran zababbun jami’an gwamnati, damar bayyana goyon bayansu ga gwamnan na ɗan lokaci.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin dabarar rage matsin lambar halin da suke ciki da kare jami’an da ke cikin barazana, tare da kiyaye sahihancin tafiyar gaba ɗaya.
Ya ce: “Mun san cewa ba a ma buga gangar siyasar 2027 ba. Magoya bayanmu su kasance a shirye. Mun san su duk inda suke, kuma su ma sun san mu. Ina ganin wannan zai taimaka wajen rage tashin hankali a jihar, musamman ga waɗanda ke cikin matsin lamba da barazana,” in ji shi.
Ya gode wa gwamnan bisa yabon da ya yi wa nasarorin gwamnatinsa a fili.
Ya ce: “Ina so in gode wa gwamnan jihar, wanda jiya ya yaba da gwamnatarmu kuma ya fallasa gwamnatin da ta lalata abubuwa da dama a jiharmu,” in ji Kwankwaso.
Dogon lissafi Kwankwaso yake yi – Na al’ada
Yayin da yake mayar da martani kan umarnin na Kwankwaso, wani masanin siyasa kuma malami mazaunin Kano, Dr Kabiru Sufi, ya ce tsohon gwamnan yana amfani da dabarar dogon lissafi ce, yana fifita tasiri na gaba fiye da yin takaddama nan take.
Ya ce: “Ina ganin wannan dabara ce ta ƙirƙirar sassauci a cikin tafiyar. Ko da mutane da dama suka bi gwamnan zuwa APC, masu lura za su ɗauka wucin gadi ne ba rasa magoya bayan tafiyar ba,” in ji Sufi.
Ya ce wannan mataki na iya rikita masu nazari da ke ƙoƙarin tantance wacce ɓangare a cikin Kwankwasiyya zai fi samun magoya baya.
Ya ce: “Da wannan umarni, ko da waɗanda suka bi gwamnan zuwa APC sun fi yawa fiye da waɗanda suka rage, mutane za su ɗauka sakamakon wannan umarni ne, ba raunin tafiyar ba. Kwankwaso ya ba wa magoya bayansa ’yancin yin shawara a ƙarƙashin matsin lamba, amma har yanzu yana da damar jagorantar su a nan gaba,” in ji Dr Sufi.
Masanin ya bayyana wannan dabara a matsayin dogon wasa na siyasa da aka tsara don kiyaye tasiri da haɗin kai a cikin tafiyar Kwankwaso kafin zaɓen 2027.
APC Kano na jiran fadar shugaban ƙasa kan ranar sauya sheƙar gwamna
A halin yanzu, APC a Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Gwamna Yusuf da sauran ’yan siyasa, tana mai cewa tana jiran fadar shugaban ƙasa ta saka rana.
Sakataren jam’iyyar na jihar, Ibrahim Zakari Sarina, ya bayyana haka jiya a cikin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust.
Ya ce a jam’iyyance, suna na’am da duk wani abu da zai karfafa su kuma ya taimaka musu wajen samun nasara a zabe mai zuwa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link