Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Gwamnatin Jamus

[ad_1]

Duk ta yadda duniya ta kara rikicewa da kuma samun sauye-sauye, haka nan Sin da Jamus ya dace su bukaci inganta tuntubar juna bisa manyan tsare-tsare, da kara amincewa da juna, da kuma karfafa samun sabon ci gaba na hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yayin da yake ganawa da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, a birnin Beijing yau Laraba.

Ya ce, yanayin da ake ciki a duniya a yanzu yana fuskantar sauyi mafi girma da ba a ga irinsa ba tun bayan karshen yakin duniya na biyu.

Shugaba Xi ya ce, ya kamata Sin da Jamus su goyi bayan babbar rawar da Majalisar Dinkin Duniya ke takawa, su sake farfado da karfinta na jagoranci, sannan su jagoranci zama masu kare tsarin mabambantan bangarori, kana masu bin doka da oda a duniya, kuma masu kare ’yancin cinikayya, da kuma kasancewa masu fafutukar nuna goyon baya da samun hadin gwiwa.

Xi ya kuma bayyana matsayin Sin game da rikicin Ukraine, yana mai cewa neman mafita ta hanyar tattaunawa da shawarwari shi ne mabudin warware batun. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *