Amnesty ta nuna damuwa kan yadda ake kama masu sukar Gwamnatin Kano
[ad_1]
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam (Amnesty International), ta bayyana damuwarta kan yadda ake yawaitar kama masu adawa da Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf.
A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Laraba, ƙungiyar ta ce Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ce, ke kama mutanen da suka bayyana ra’ayoyin da suka saɓa da na gwamnati.
A cewar Amnesty, wannan yanayi na haifar da tsoro tare da taƙaita ’yancin jama’a na faɗin albarkacin bakinsu a jihar.
Daga cikin misalan da ta bayar akwai Abba Ibrahim Hussain, ɗalibin sashen shari’a a Jami’ar Northwest, wanda aka ce jami’an DSS sun tsare sakamakon sukar gwamnan jihar.
“Har yanzu yana tsare, kuma akwai yiwuwar ba zai samu damar zana jarabawarsa da ake yi a yanzu.
“Haka kuma, an tsare wani matashi da ya yi fice a kafafen sada zumunta, Aminu Warkal, na tsawon sa’o’i biyar bisa zargin cin zarafin gwamna,” in ji Amnesty.
Ƙungiyar ta kuma ce an gayyaci Samir Hanga zuwa ofishin DSS domin yi masa tambayoyi saboda sukar gwamnatin Kano.
Hakazalika, ta ce an kama Abdulmajid Danbilki Kwamanda makonni biyu da suka wuce, inda aka matsa masa ya janye kalaman da ya yi a kan Gwamna Abba.
Ta ƙara da cewa an tsare Saifullahi Abubakar saboda yin wani bidiyon barkwanci a shafin TikTok game da gwamnan.
Amnesty ta bayyana waɗannan matakai a matsayin cin zarafi, inda ta jaddada cewa sukar jami’an gwamnati ba laifi ba ne.
“Babu wanda ya fi ƙarfin a soke shi kowane muƙami ne da shi. Kama ’yan adawa take haƙƙin ’yancin ɗan Adam ne,” in ji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta ce kaf faɗin Najeriya ana ci gaba da samun mutane da ke amfani da kafafen sada zumunta wajen tattauna harkokin siyasa da mulki, amma a Jihar Kano, lamarin ya sha bamban.
Amnesty ta buƙaci hukumomi su mutunta tare da kare ’yancin faɗin albarkacin baki.
Ta yi gargaɗin cewa irin wannan mataki na gwamnatin Kano na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya da harkokin jama’a.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link