Yadda Wani Matashi Ya Kashe Abokin Aikinsa A Fadar Gwamnatin Gombe

[ad_1]

Rundunar Ƴansandan Jihar Gombe ta kama wani matashi ɗan shekara 19 mai suna Shuaibu Adamu, bisa zargin kashe wani abokin aikinsa, Malam Umar, a harabar Fadar Gwamnatin Jihar Gombe. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 26 ga Disamba, 2025, inda dukkaninsu ke aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi.

Kakakin ƴansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:50 na yamma cewa an tsinci Malam Umar, wanda aka fi sani da “Baba Usama”, ba ya motsi. Nan take aka garzaya da shi zuwa Asibitin Kwararru na Gombe, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa. Marigayin yana aiki ne a matsayin mai kula da rijiyar burtsatse a fadar gwamnatin.

  • Kirsimeti: Gwamnan Gombe Ya Karɓi Baƙuncin Kiristoci
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Binciken farko ya nuna cewa mutuwar ta kasance mai cike da shakku, lamarin da ya sa Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike. Bayan duba faifan bidiyon CCTV ya nuna cewa an kai wa marigayin hari ne jim kaɗan kafin mutuwarsa daga hannun wani abokin aikinsa, Shuaibu Adamu.

Ƴansanda sun ce wanda ake zargin ya tsere bayan faruwar lamarin, amma an bi sawunsa tare da kama shi da misalin ƙarfe 11 na dare a unguwar Bagadaza dake Gombe. An bayyana cewa ya amsa laifinsa yayin tambayoyin farko. An ajiye gawar marigayin a ɗakin ajiyar gawarwaki domin yin binciken likita, yayin da ake ci gaba da bincike a kan lamarin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *