Yara 5 sun rasu bayan cin guba a abinci a Taraba
[ad_1]
Yara biyar sun baƙunci lahira yayin da wasu takwas ke kwance a asibiti bayan sun ci guba a cikin abinci a garin Takum da ke Jihar Taraba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Victor Mshelizah, ya ce yaran sun ci nama, wanda ake zargin an sa guba a ciki yayin da suke karatun azumi a ranar Talata.
A cewarsa, yara biyar sun rasu bayan cin naman, yayin da aka garzaya da wasu takwas asibiti domin kula da su.
Hukumomi sun fara bincike domin gano ainihin abin da ya jawo lamarin.
’Yan sanda sun buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abun zargi, ko rashin lafiya ga jami’an tsaro domin kauce wa tashin hankali.
Wani lauyan kare haƙƙin ɗan Adam da ke zaune a Jalingo, Bilyaminu Maihanci, ya nuna alhininsa kan rasuwar yaran.
Ya yi kira ga gwamnati, ’yan sanda da ma’aikatar lafiya su yi bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.
Ya ce iyalan waɗanda suka rasu sun cancanci adalci, yaran da ke asibiti suna buƙatar kulawa ta musamman.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link