Jami’in Afirka Ta Kudu: Jarin Da Sin Ta Zuba Ya Ba Da Gudummarwar Samar Da Guraben Aikin Yi

[ad_1]

A ranar Litinin, wani jami’in kasar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, jarin da kasar Sin ta zuba a lardin Gauteng na kasar Afirka ta Kudu, ya ba da gudumammawar samar da guraben aikin yi da yawa a wurin, tare da shigo da fasahohin kere-kere masu ci gaba.

A yayin da yake jawabi game da yanayin lardin Gauteng, gwamnan lardin Panyaza Lesufi ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin sun zuba jari kan wasu nau’ikan sana’o’in lardin, lamarin da ya taka rawar raya tattalin arzikin lardin.

Ya kuma kara da cewa, kamfanin Chung Fung Metal na kasar Sin ya zuba jari na dallar Amurka miliyan 156 domin kafa wata sabuwar ma’aikatar sarrafa karafa, tun daga watan Janairu na bana, wato lokacin da ma’aikatar ta fara aiki, ya zuwa yanzu, ta riga ta samar da guraben aikin yi sama da 1000. (Mai Fassara: Maryam Yang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *