Da Ɗumi-ɗumi: Disu Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Muƙaddashin Sufeto Janar
[ad_1]
Shugaban ‘Yansanda na riƙo, Tunji Disu, ya karɓi ragamar aiki a ranar Laraba.
Hakan ya biyo bayan ado da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa a yau a fadar shugaban kasa.
- Ayyukan Tattalin Arziki Na Matsakaita Da Kananan Kamfanonin Sin a 2025 Sun Gudana Ba Tare Da Tangarda Ba
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 8
Kayode Egbetokun, wanda aka naɗa a ranar 19 ga Yuni, 2023, ya yi murabus daga muƙaminsa ranar Talata, wanda hakan ya sanya aka naɗa Disu.
Disu ya karɓi gaisuwar girmamawa ta farko a matsayin Sufeto Janar daga jami’an ‘yansanda a Hedikwatar ‘Yansanda bayan ya dawo daga Villa da misalin ƙarfe 4:25 na yamma.
Daga nan, Egbetokun da Disu suka tafi cikin ofishi domin shirin miƙa ragamar aiki a hukumance.
[ad_2]
Source link