Ayyukan Tattalin Arziki Na Matsakaita Da Kananan Kamfanonin Sin a 2025 Sun Gudana Ba Tare Da Tangarda Ba

[ad_1]

Bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin sun nuna cewa, a shekara ta 2025 ayyukan tattalin arziki na matsakaita da kananan kamfanoni na kasar Sin sun gudana ba tare da tangarda ba, inda suka nuna karfin juriya mai karfi, kuma suka zama muhimmin abin dogaro ga bunkasar tattalin arzikin masana’antu.

A shekara ta 2025, yawan karuwar darajar matsakaita da kananan kamfanonin masana’antu masu karfi ya karu da kashi 6.9 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2024, wanda ya fi na jimillar karuwar darajar daukacin kamfanonin masana’antu yawa da kashi 1.0 cikin 100, shekaru 3 ne da aka samu karuwar. Kudaden shiga na matsakaita da kananan kamfanonin masana’antu sun kai Yuan tiriliyan 83.8, wadanda suka karu da kashi 2.6 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2024. Jimillar ribarsu ta karu da kashi 1.4 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2024, musamman ma jimillar ribar masana’antun kera kayan aiki ta ci gaba da karuwa cikin sauri, inda ta karu da kashi 11.4 cikin 100.

A shekara ta 2025, darajar kamfanonin kere-kere na musamman masu karfi da rinjaye a bangaren kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha, ta karu da kashi 9.0 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024, kuma jimillar ribarsu ta karu da kashi 7.0 cikin 100.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *