Binciken CGTN: 80% Na Matasan Duniya Sun Yi Kiran Maida Hankali Kan Karin Kasafin Kudin Tsaron Kasar Japan
[ad_1]
Majalisar ministocin kasar Japan ta zartas da shirin kasafin kudi kan tsaron kasa na shekarar 2026 a yau 26 ga wannan wata, wanda yawansa ya kai kudin Japan triliyan 9. Idan majalisar dokokin kasar Japan ta zartas da wannan shiri a farkon badi, wannan kasafin kudi kan tsaron kasar Japan zai zama mafi yawa a tarihinta.
Bayan da firaministar kasar Japan Sanae Takaichi ta bayyana jerin ra’ayoyinta na saba wa tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu, masu tsattauran ra’ayi na kasar Japan sun gaggauta karfafa ayyukanta na soja, da kawo illa ga kasa da kasa a wannan fanni.
Kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ta gabatar da kuri’ar jin ra’ayoyi ga mutanen kasa da kasa 17,043. A cikinsu kashi 81.5 cikin dari sun bayyana cewa, Sanae Takaichi ta riga ta zama mai sauya tarihi da tada zaune-tsaye da kawo illa ga zaman lafiya da kuma tada rikici.
Ya kamata kasa da kasa su maida hankali kan masu tsattsauran ra’ayi na kasar Japan bisa yunkurinsu farfado da ra’ayin karfin soja, kana kashi 83 cikin dari na masu jefa kuri’un daga shekaru 18 zuwa 44 sun fi maida hankali ga wannan batu. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link