Kotu Ta Sake Ci Gaba Da Shari’ar ‘Yan Bindiga Biyar Masu Alaka Da Bello Turji

[ad_1]

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na sake bude tuhumar ta’addanci kan wasu mutane biyar da ake zargi da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji.

Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, ya amince da bukatar da babban mai shari’a na kasa (AGF) ya gabatar na neman a sake shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CR/633/2024, a jerin dalilan kotun.

  • Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami
  • Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno

An dai ci gaba da shari’ar ne, a ranar 8 ga watan Yulin 2025, bayan lauyan da ke kare wanda ake tuhuma ya nemi a kori karar, saboda zargin rashin gurfanar da shi a gaban kotu.

Mai gabatar da kara, ta bakin lauyan AGF, Dabid Kaswe, ya bayar da hujjar cewa; masu gabatar da kara ba su kare dage zaman da aka yi ba, sannan kuma a shirye suke tsaf, domin gabatar da shaidu.

Laifukan ta’addanci 11 da aka shigar a farko a ranar 16 ga watan Disamba, 2024, ya shafi mutane takwas da ake tuhuma da suka hada da Musa Muhammed Kamarawa, Abubakar Hashimu (wanda aka fi sani da Dakta), Bashir Abdullahi, Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma, wadanda a halin yanzu suke tsare. Sai dai, Bello Turji da Aminu Muhammad da Sani Lawal suna nan a matsayin manyan jagororinsu.

Ana zargin wadanda ake zargin da bayar da tallafin kayan aiki ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da Turji ke jagoranta da sauran ‘yan fashi da suka hada da samar da haramtattun kwayoyi, abinci, kayan soja da na ‘yansanda, kayayyakin gine-gine, har ma da samar da wata motar yaki da ake amfani da ita wajen ayyukan ta’addanci.

A yayin shari’ar, Kaswe ya ci gaba da cewa; rashin halartar masu gabatar da kara a ranar 8 ga watan Yuli, ya faru ne sakamakon wani aiki a hukumance; ba da gangan ba, yana mai jaddada muhimmancin sake shigar da karar, domin tabbatar da adalci, tsaron kasa da kare lafiyar jama’a.

Lauyan wadanda ake kara na 1 da na 2, Lukman bai yi adawa da bukatar ba, sai dai ya bukaci a biya shi Naira miliyan 10 a kan masu gabatar da kara, saboda tsawaita tsare wadanda ake tuhuma a lokacin shari’ar.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Nwite ya bayyana cewa; bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar, ta dace kuma ta amince da shi, inda ta ba da umarnin a ci gaba da shari’ar ba tare da biyan wasu kudade ba.

An dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 21 ga watan Janairun 2026.

Shari’ar dai, ta bayyana kokarin da hukumomin Nijeriya ke ci gaba da yi na gurfanar da ta’addanci a sassan duniya da kuma karfafa daukar nauyin tallafin kayan aiki ga haramtattun kungiyoyi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *