Iyayen Marayu 501 Ne Suka Samu Tallafin Abincin Azumi Daga Dan Amo A Kano
[ad_1]
Iyayen marayu 501 suka samu tallafin kayan abincin azumin watan Ramadan daga Alhaji Aminu Mukhatr Dan Amo, wanda ya zaBo gidajen marayu a unguwanni na birnin Kano domin tallafa musu da kayan abinci.
Kayayyakin abincin sun hada da shinkafa da mai domin rage musu radadin rashin iyaye da rage tsananin da ake ciki a wannan hali a Nijeriya.
- Sharuɗan Da Chelle Ya Gindaya Wa NFF Domin Cigaba Da Jagorantar Super Eagles
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 3
Tun da farko a jawabinsa, Alhaji Dan Amo ya ce shi a matsayinsa na wanda ya taso a maraici, ya dubu wannan hali ne da kuma umarnin Ubangiji na ce wa duk wanda ya samu hali ya taimaka wa mara hali, domin duk wanda ya kwana da yunwa, to Ubagiji zai tuhumi wanda yake da hali.
A karshe, ya gode wa Ubangiji kan wannan dama da ya ba shi, sannan ya yaba wa daukacin mahalarta taron raba tallafin irinsu tsohon gwamna Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da jami’an gwamnati da sauran al’umma da suka halartci wannan taro.
Ya nemi shugabanni da sauran al’umma, musamman mawadata da su yi iya kokarinsa wajen tallafa wa marayu da raunana, domin hakan garkuwa ce daga dukkanin masifu da kuma bunkasar tsaro da tatatalin arziki a tsakanin al’umma.
[ad_2]
Source link