Zargin Kutse: DSS za ta gurfanar da El-Rufai a kotu a ranar 25 ga Fabrairu

[ad_1]



Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) na shirin gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotu a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Za ta gurfanar da shi a Babbar Kotun Taratya da ke Abuja, inda mai shari’a Joyce Abdulmalik za ta saurari shari’ar.

DSS ta shigar da tuhume-tuhume uku a kansa, inda ta ke zarginsa da yin kutse a wayar Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

Hukumar ta ce hakan ya saɓa dokokin laifukan na Intanet da sadarwa na Najeriya.

Tun da farko, Hukumar EFCC ta tsare shi kan wasu laifuka da suka da ake zarginsa da aikatawa a lokacin da yake mulki.

Bayan EFCC ta bayar da belinsa, Hukumar ICPC ta cafke shi domin yin bincike kan zargin cin hanci a lokacin da yake gwamna.

Sabbin tuhume-tuhumen sun biyo bayan wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise, inda ya ce shi da wasu sun yi kutse a wayar NSA kuma ya ji lokacin da Ribadu ya bayar da umarnin kama shi.

Hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani ba, amma sun ce abin da ake zargin sa da shi ya saɓa wa doka.

A halin yanzu, El-Rufai na hannun ICPC, kuma za a gurfanar da shi a kotu a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *