An Dakatar Da Chelsea Daga Sayen ‘Yanwasa

[ad_1]

Hukumar kula da gasar firimiya ta Ingila ta sanyawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tara mafi kololuwa da ta taba cin wata kungiya mai haskawa a gasar mafi girma a Ingila, bayan da aka nemi ta biya kudin da ya kai fam miliyan 10 da dubu 750 kodayake an janye mata haramcin sayen ‘yan wasa dangane da tuhumar da ake mata kan cinikayyar ‘yan wasa a bayan fage da kuma boye farashinsu.

Hukumar firimiyar ta ce bincikenta ya gano cewa Chelsea ta yi wannan haramtacciyar harkalla ne a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2018 ta yadda cikin sirri ta yi hulda da wasu dillalan ‘yan wasa marasa rijista don shiga tsakani a cinikin ‘yanwasan da ta yi a wancan lokacin kuma babban laifi ne a dokar hukumar kwallon Ingila.

  • ADC – Jafaru Sani Ya Mika Sakon Barka Da Sallah, Ya Soki Tsare El-Rufai
  • Ministan Tsaron Nijeriya Ya Taya Al’ummar Musulmai Murnar Sallah

Bayanai sun ce Chelsea ta ma samu sassauci ne haka zalika hukumar ta kau da kai duba da yadda kungiyar ta bayar da hadin kai wajen bincike tare da amsa laifinta, hakan ya sanya ba a kai ga rage mata maki ko kuma yin kasa da darajarta ba. Firimiya ta wallafa wasu bayanai masu shafi 28 dauke da dukkanin laifukan na Chelsea da kudin da ta kashe wajen kawo ‘yan wasan dama ‘yan wasan har da dillalan marasa rijista da aka biya kudin.

Wasu daga cikin ‘yanwasan da Chelsea ta biya Fam miliyan 47 da rabi ta bayan fage wajen kawo su sun kunshi Eden Hazard daga Lille kana Ramires daga Benfica sai Dabid Luis shima daga Benfica sannan Andre Schurrle daga Bayer Leberkusen sai kuma Nemanj Matic wanda kungiyar ta saya daga dai  Banfica.

Ka zalika akwai kudaden cinikin Samuel Eto’o da Williams da kuma Anzhi Makhachkaa dukkaninsu ta bayan fage da aka biya fam miliyan 19 da adubu 300. Sannan an dakatar da kungiyar ta Chelsea daga sayan matasan ‘yanwasa wadanda za su dinga bugawa a karamar kungiya na watanni tara, sakamakon samun Chelsea da karya dokar sayan matasan ‘yanwasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *