NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU
[ad_1]
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni huɗu domin ta warware duk wata tankiya da ke tsakaninta da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da sauran ƙungiyoyin jami’o’i da na manyan makarantu.
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da ’yan jarida a Labour House da ke Abuja.
Ajaero ya ce, idan gwamnati ta gaza kammala tattaunawa da ƙungiyoyin cikin wa’adin da ta bayar, NLC ba za ta yi wata-wata ba wajen ɗaukar matakin da ya dace ta hanyar amfani da dukkan wani tanadi da doka ta yi.
Ya kuma bayyana cewa sun gano cewa wasu ƙungiyoyin haɗin gwiwa a ƙarƙashin NLC suna ganawa da jami’an gwamnati ba tare da izini ko umarni daga uwar ƙungiya ba, wanda shi ne dalilin da ya sa yarjejeniyoyi da dama ba a cika su ba.
Jawabin da Kwamared Ajaero ya yi na zuwa ne bayan taron da NLC ta yi da shugabannin ƙungiyoyin jami’o’i ciki har da ASUU, SSANU, NASU da NAAT.
A makon da ya gabata ne ASUU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, bayan ƙarewar wa’adin na kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati, dangane da batutuwan da suka shafi walwala da jin daɗin ma’aikata, albashi, da aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009.
Sai dai Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce bai kamata ASUU ta shiga yajin aiki ba, domin a cewar tattaunawa ta ta yi nisa, kuma gwamnati ta saki Naira biliyan 50 na kuɗaɗen alawus ɗin malaman jami’o’i, tare da ware Naira biliyan 150 a cikin Kasafin 2025 domin gyaran jami’o’in.
A yayin taron da NLC ta gudanar, Kwamared Ajaero ya jaddada cewa daga yanzu, ƙungiyar ƙwadago ko wata ƙungiya a ƙarƙashinta ba za ta sake ganawa da jami’an gwamnati ba tare da izini ba, musamman waɗanda ke da alhakin aiwatar da yarjejeniyoyin da ake sanya hannu a kai.
Ya kuma soki matakin da gwamnatin ta ɗauka na amfani da dokar “ba aiki, ba albashi” kan mambobin ASUU yana mai cewa:
“Mun yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin mako huɗu domin ta kammala dukkan tattaunawa a wannan bangare. Mun fara da ASUU, amma matsalolin sun wuce na ASUU kaɗai.
“Idan bayan mako huɗu ba a kammala komai ba, za mu kira taron gaggawa na ƙasa domin ɗaukar matakin gama-gari, wanda dukkan ma’aikata da ƙungiyoyi a faɗin ƙasa za su shiga ciki.”
Ya ƙara da cewa, “Zamanin sanya hannu kan yarjejeniyoyi da yi wa ƙungiyoyin da ke neman haƙƙinsu barazana ya ƙare.
“Wannan batu na ‘ba aiki, ba albashi’ daga yanzu zai zama ‘ba albashi, ba aiki’. Saboda mun gano cewa fiye da kashi 90 cikin 100 na yajin aikin da ake yi a ƙasar nan na faruwa ne saboda rashin cika ƙa’idar yarjejeniyoyi.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link