Majalisar NPC Ta Gudanar Da Zaman Rufe Taronta Na Shekara-shekara Na Bana
[ad_1]
A yau Alhamis ne majalisar wakilan jama’ar kasar Sin(NPC) ta 14, ta gudanar da zaman rufe taronta na shekara-shekara, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran shugabannin jam’iyyar kwaminis ta kasar da shugabannin kasar suka halarci taron a babban zauren taruwar jama’a dake birnin Beijing.
Yayin zaman, ‘yan majalisar wakilan sun zartar da kuduri game da rahoton aikin gwamnati, tare da amincewa da kundin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15, wanda za a aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2026 zuwa 2030, domin bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummun kasar ta Sin. Kana sun kada kuri’ar amincewa da dokar kare muhallin halittu da muhalli, da ta inganta hadin kan kabilun kasa da yayata ci gabansu, da kuma dokar kasa ta tsara dabarun ci gaba. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link