Sojoji sun kashe Kwamandan ISWAP da mahara a Yobe
Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas (OPHK) sun kashe aƙalla membobin Boko Haram/ISWAP 20, ciki har da wani babban Kwamandan su mai suna Abu Yusu, Munzir na Dursula, a wasu hare-hare da suka yi yunƙurin kaiwa kan al’ummar Goniri a ƙaramar hukumar Gujba, jihar Yobe.
Hare-haren, waɗanda suka fara a daren Litinin, 9 ga Maris 2026, kuma suka ci gaba har zuwa safiyar Talata, 10 ga Maris 2026, sun kai hari kan sansanonin sojoji a ƙarkashin sashe na 2 na Operation HADIN KAI (OPHK).
Majiyar na cewar, wasu sojoji sun samu raunuka a lokacin fafatawar amma an kwashe su nan take kuma a halin yanzu suna cikin kwanciyar hankali.
An tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da Laftanar Kanar Sani Uba, jami’in yaɗa labarai na OPHK ya fitar, yadda ya ce sojoji sun yi nasarar daƙile ƙoƙarin da ‘yan ta’addan suka yi, wanda ya haɗa da ci gaba da mamaye ƙauyen Goniri da kuma mahaɗar Ngamdu a wani yunƙuri na kewaye sansanonin sojoji.
“Sojojin da ke cikin shirin sun mayar da martani da sauri da ƙarfin wuta da dabarun yaƙi, suna daidaita tsaron su yayin da aka tura ƙarin sojoji da tallafin mayaƙan sama,” in ji Laftanar Kanar Uba.”
“‘A cewarsa ‘yan ta’addan sun gaji inda suka tilasta musu ja da baya cikin ruɗani da ƙarfin wuta, suna fuskantar mummunan rauni, ciki har da babban Kwamandan su da ya riga mu gidan gaskiya.”
Bayan rikicin, sojoji sun gano gawarwaki da dama, makamai, harsasai, na’urorin fashewa (IEDs) da sauran kayan aiki na ‘yan ta’addan da suka tsere suka yi watsi da su.
samamen da aka kai a Triangle na Timbuktu, musamman a kusa da Gwaigomari, sun haifar da gano ƙarin asarar rayukan ‘yan ta’adda.
Laftanar Kanar Uba ya jaddada cewa, a yanzu haka yankin yana ƙarƙashin ikon sojoji kuma sojojin ƙasa da na sama suna ci gaba da ayyukan bin diddigi masu ƙarfi a cikin al’ummomin da ke kewaye don gano duk wani ɗan ta’adda da ya tsira.
Ya ƙara da cewa, “Operation HADIN KAI ta ci gaba da jajircewa wajen kawar da ta’addanci gaba ɗaya da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a duk faɗin Arewa maso Gabas.
“Babban Kwamandan Soja ya yaba wa sojojin saboda jarumtakar su da juriyarsu yayin da yake kira gare su da su ci gaba da aiki tukuru.”