Iran Ta Kama Mutane Kusan 200 Kan Zargin Yi Wa Amurka Da Isra’ila Leƙen Asiri
[ad_1]
Hukumomin Iran sun kama kusan mutane 200 da ake zargi da yi wa Amurka da Isra’ila leƙen asiri a lokacin da ake yaƙi tsakanin ƙasashen.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama mai suna Human Rights Activists News Agency ta ce an kama mutane 195 a birnin Tehran da wasu birane, ciki har da Tabriz.
- NNPC Ta Rage Farashin Fetur
- Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP, Sun Kashe ’Yan Ta’adda 20 A Yobe
A cewar ƙungiyar, an kama mutanen ne saboda zargin suna amfani da kafofin sada zumunta wajen aike hotuna da bidiyon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a Iran zuwa kafafen yaɗa labarai na duniya.
Rahotanni sun ce rundunar sojin Iran ma ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da aika bidiyon hare-haren zuwa kafafen labarai na waje.
An kuma nuna su a talabijin suna amsa laifinsu.
Shugaban rundunar ’yansandan ƙasar, Ahmad Reza Radan, ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya shiga zanga-zanga a wannan lokaci za a ɗauke shi a matsayin mai cin amanar ƙasa.
Hukumomin ƙasar sun kuma yi gargaɗi ga iyaye da su hana ’ya’yansu shiga zanga-zanga a ciki ko wajen ƙasar yayin da Iran ke ci gaba da gwabza yaƙi.
Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin da Amurka da Isra’ila ke yaƙi da Iran.
[ad_2]
Source link