An Yi Taron Dandalin Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Beijing
An gudanar da taron dandalin tattaunawar masana na jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS, da jam’iyyar Kuomintang wato KMT a birnin Beijing a yau Talata 3 ga wannan wata, wanda cibiyar nazarin dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan ta ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na JKS da asusun nazarin harkokin jam’iyyar KMT suka dauki bakunci tare, inda wakilai da masana daga jam’iyyun biyu, da bangarorin masu yawon shakatawa, da masana’antu, da jami’an kiwon lafiya, da na kiyaye muhalli da sauransu fiye da 100 suka halarci taron.
Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na JKS Song Tao ya yi jawabi a gun bikin bude taron dandalin cewa, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ya taya murna ga Cheng Li-wun da ta zama shugabar jam’iyyar KMT, kuma batun ya nuna taswira ga raya dangantakar dake tsakanin jam’iyyun biyu da gabobin biyu.
Mahalarta taron dandalin sun tattauna batutuwan mu’amala da hadin gwiwa a fannonin yawon shakatawa, da sana’o’i, da kiyaye muhalli da hadin gwiwa mai dorewa. Mahalartan sun amince da ma’ana da amfanin gudanar da dandalin tattaunawar, inda suka yi tsammanin cewa, mu’amalar dake tsakanin jam’iyyun biyu za ta taimaka wa zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, da amfanar da jama’arsu baki daya.
Kazalika, sun yi kira ga bangarori daban daban na gabobin biyu da su yi kokari tare don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin gabobin biyu da kiyaye zaman lafiya da kawar da cikas a tsakaninsu don samar da kyakkyawan yanayin zurfafa mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu baki daya. (Zainab Zhang)