Gwamnan Sakkwato Ya Mayar Da Malaman Islamiyya Ma’aikata Ya Rabawa Mahaddata Babura

[ad_1]

Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya bayar da umurnin daukar malaman makarantar Ma’ahadut Tahfizi Waddarasatul Qur’aniyya 53 aiki a matsayin ma’aikatan gwamnatin jiha nan take.

Gwamnan ya umurci ma’aikatar lamurran addini da ta hada hannu da ma’aikatar kudi domin tabbatar da saka malaman a cikin tsarin albashi daga watan maris.

Haka ma gwamnatin ta bayar da kyautar babura 259 ga daliban da suka haddace Alkur’ani a bikin yaye mahaddatan.

A cewar Gwamnan ba wai suna murnar kammala haddar Alqur’anin daliban ba ne kawai ba suna kuma murnar sadaukarwa, jajircewa ladabi da biyayya da himmatuwa ga koyarwar ubangiji.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *