Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin N1.477trn na 2026

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira tiriliyan 1.477.

Bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Abba, ya yi kira ga mambobin majalisar zartarwa su ƙara jajircewa wajen cimma burin gwamnati.

Ya nuna cewa kasafin shekarar 2025 ya samu nasarar aiwatar da sama da kashi 80 cikin 100, musamman a fannin ilimi, lafiya, da manyan ayyukan ci gaba.

“Kasafin da aka gyara ya haɗa muhimman buƙatun ci gaban ababen more rayuwa, kuma mun shirya sosai don aiwatar da shi don amfanar al’ummar Kano,” in ji gwamnan.

Tun da farko an ƙiyasta kasafin 2026 zuwa Naira tiriliyan 1.3, amma Majalisar Dokokin jihar ta ƙara shi zuwa Naira Tiriliyan 1.477.

Kashi 71 cikin 100 na kuɗin za a kashe shi ne wajen gudanar da manyan ayyukan ci gaba, yayin da kashi 29 cikin 100 zai tafi ɓangaren gudanarwa.

Gwamnan, ya kuma bayyana shirin girmama wasu mambobin majalisar dokoki biyu da suka rasu a yayin gudanar da aiki, inda ya bayyana rasuwarsu a matsayin babban rashi ga jihar.

“Za mu tabbatar cewa duk kuɗaɗen da aka ware a kasafin za a yi amfani da su yadda ya kamata domin tasirin manufofinmu ya shafi dukkanin mazauna Kano,” in ji shi.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore, ya ce majalisar ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ma’aikatun gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki kafin amincewa da kasafin.

Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa kasafin da aka gyara zai inganta ci gaban tattalin arziƙi da walwalar mazauna jihar idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *