Gwamna Yusuf Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kuɗi Na 2026 Na Naira Tiriliyan 1.47

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudin 2026 na Naira Tiriliyan 1.47

Gwamnan ya rattaba hannu kan kasafin kudin ne a ranar Laraba yayin wani taron Majalisar Zartarwa ta Jihar (SEC) da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.

  • Ba Mu Da Shirin Mayar da Nijeriya Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya – APC
  • Peter Obi Da Shugabannin Kudu Maso Gabas Sun Koma Jam’iyyar ADC A Enugu

Kasafin kudin, wacce ta kai Naira Tiriliyan 1,477,829,666,131, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ita a makon da ya gabata a lokacin zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Alhaji Ismail Falgore ya jagoranta.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya gabatar da kiyasin kasafin kudin Naira Tiriliyan 1,368,127,929,271 ga Majalisar a makon da ya gabata.

A cewar gwamnan, kasafin kudin 2026 an tsara shi ne don ci gaba da ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa, da kuma saka tallafi a manyan sassan tattalin arzikin jihar, tare da mai da hankali kan bunkasa ababen more rayuwa, ci gaban tattalin arziki mai hade da ci gaba mai dorewa da juriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *