2027: APC na iya fuskantar ƙalubale idan ta sauya Shettima — Musawa
[ad_1]
Ministar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musawa, ta yi gargaɗin cewa jam’iyyar APC na iya fuskantar matsala a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 muddin ta cire Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, daga tikitin takara tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Musawa wadda ta yi wannan tsokaci yayin wata hira da da fitaccen ɗan jaridar nan, Seun Okinbaloye , ta ce cire Shettima ko maye gurbinsa da wanda ba Musulmi ɗan Arewa ba na iya janyo babbar matsala ga APC, musamman a jihohin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma, inda siyasa ke da matuƙar tasiri a rayuwar al’umma.
Ta bayyana cewa sauya tsarin tikitin Musulmi-da-Musulmi da APC ta yi amfani da shi a 2023 na iya haifar da koma baya, tana mai cewa masu ba da shawarar hakan ba su fahimci yanayin siyasar Arewa yadda ya kamata ba.
“Jihohin Arewacin Najeriya ginshiƙai kamar Katsina, Kano, Kaduna, Kebbi, Jigawa, Zamfara da Sakkwato sun fahimci siyasa sosai.
“A waɗannan jihohin mutane sun mayar da siyasa tamkar rayuwa, inda jama’a ke jira duk bayan shekara huɗu su koma layin zaɓe su kaɗa ƙuri’a, domin a nan ne suke jin suna da wani tasiri,” in ji ta.
Musawa ta yi watsi da iƙirarin cewa jam’iyyar APC na iya sauya tikitin takarar shugaban ƙasa cikin sauƙi ba tare da fuskantar wata matsala ba, tana mai bayyana irin wannan tunani a matsayin rashin fahimtar siyasa.
Haka nan, wani jigo a APC, Farfesa Haruna Yerima, ya gargaɗi jam’iyyar da kada ta taɓa tikitin Tinubu/Shettima, yana mai cewa duk wani yunƙurin sauya shi na iya jefa APC cikin babbar matsala a 2027.
Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, Bala Ibrahim, ya ce bai kamata addini ya zama ginshiƙin lissafin siyasa ba, yana mai jaddada cewa cancanta, amana da ikon cika alƙawari su ne muhimman abubuwan da masu kaɗa ƙuri’a ke dubawa, ba addini kaɗai ba.
A daina yaɗa jita-jitar sauya Shettima — APC
Tuni dai jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar za ta sauya Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu a Zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce rahotannin ba su da tushe, “kuma tsantsar jita-jita ce da ke da nufin haddasa ruɗani da rikici a harkokin siyasar ƙasar.”
APC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Felix Morka, ya fitar.
Bayanai sun ce an daɗe ana raɗe-raɗin cewa jam’iyyar APC za ta iya sauya mataimakin shugaban ƙasar gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
Tun farkon haɗin Bola Tinubu da Kashim Shettima ya sha suka daga wasu ɓangarorin ƙasar kasancewar ana ganin hakan ya saɓa da al’adar da aka saba da ita ta saɓawar addinin shugaban ƙasa da mataimakinsa.
Sai dai a lokuta da dama masu alaƙa da jam’iyyar mai mulki sun ce an yi haɗin ne a matsayin wata dabara ta siysa da neman cin zaɓe a shekara ta 2023.
Ana sa ran harkokin siyasa za su rincaɓe a cikin wannan shekara ta 2026, gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara mai zuwa, inda ake sa ran Tinubu zai sake tsayawa takara domin neman wa’adin shugabanci na biyu na tsawon shekara huɗu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link