A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Amurka Wajen Daukaka Hadin-Gwiwarsu
[ad_1]
Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta ce a shirye kasar take, ta hada hannu da Amurka, su ajiye bambance-bambancen dake tsakaninsu a gefe, domin daukaka hadin-gwiwarsu da raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai karko da aminci da dorewa a tsakaninsu.
Mataimakin ministan kula da cinikayya ta kasar Sin, Yan Dong ne ya bayyana haka a yau Litinin, yayin wani taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira.
A cewar Yan Dong, Sin da Amurka sun gudanar tattaunawa har zagaye biyar, kan tattalin arziki da cinikayya a shekarar 2025, bisa ka’idoji na daidaito da girmama juna da moriyar juna, wadanda suka samar da tarin kyawawan sakamako.
Ministan ya ce, wannan ya nuna cewa Sin da Amurka za su iya lalubo hanyoyin warware batutuwa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.
Ma’aikatar ta kuma lashi takobin a bana, za ta kara aiwatar da manufofi masu goyon bayan jarin waje, tana alkawarin kokarin bayar da kulawa iri daya ga kamfanonin cikin gida da masu jarin waje a shirye-shiryen kasar na bunkasa sayayya a cikin gida da harkokin sayayya na gwamnati da tsarin neman kwangila, domin inganta ci gaba mai dorewa ga kamfanoni masu jarin waje dake kasar. (FMM)
[ad_2]
Source link