Trump ya yi barazanar daina hulɗar kasuwanci da Sifaniya kan yaƙin Iran
[ad_1]
Shugaba Donald Trump ya yi barazanar katse duk wata hulɗar kasuwanci da Sifaniya bayan gwamnatin ƙasar ta ƙi bai wa jiragen yaƙin Amurka damar amfani da sansanoninta domin kai wa Iran hari.
Gwamnatin Sifaniya wadda ke ƙarƙashin jagorancin Firaiminista Pedro Sanchez, ta bayyana cewa sansanonin da Amurka ke amfani da su a ƙasar za a amince da su ne kawai idan ayyukan sun dace da kundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Da yake ganawa da Firaministan Jamus Friedrich Merz a Fadar White House, Trump ya ce Sifaniya ta nuna halin ko-in-kula, yana mai zargi ƙasar da hawa kujerar naƙi kan ƙara yawan kuɗaɗen tsaro zuwa kashi biyar cikin ɗari kamar yadda ya buƙata daga ƙawayen Ƙungiyar Ƙawancen Tsaro ta NATO.
“Saboda haka za mu katse duk wata hulɗar kasuwanci da Sifaniya. Ba ma son komai da ya shafe ta,” in ji Trump, inda ya ƙara da cewa ya umarci Sakataren Baitul Mali, Scott Bessent, da ya dakatar da duk wata mu’amala da ƙasar.
Sai dai ba a fayyace ikon da Trump yake da shi na dakatar da hulɗar kasuwanci gaba ɗaya ba, musamman bayan da Kotun Ƙoli ta Amurka ta soke wasu dokokin gaggawa da ya taɓa amfani da su wajen ƙaƙaba haraji.
A martanin da ta mayar, gwamnatin Sifaniya ta ce hulɗar kasuwancinta da Amurka ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka tsakanin ɓangarorin biyu.
Saboda haka Sifaniya ta jaddada cewa duk wani sauyi kan hulɗar da ke tsakaninsu dole ne ta mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin da ke tsakanin Tarayyar Turai da Amurka.
A jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin a safiyar Laraba, Sanchez ya jadadda matsayar gwamnatinsa ta hana Amurka amfani da filin jirginta domin kai wa Iran hari.
“Ba za mu goyi bayan yaƙi ba” in ji firaministan.
Ya yi kira da kada a maimaita “kurakuran da suka gabata”, yana mai nuni da mamayar da aka yi wa Iraƙi a 2003, wadda ya ce ba ta cimma manufofinta ba, sai ma ta haifar da rashin tsaro da kuma taɓarɓarewar rayuwar jama’a da dama.
Sanchez ya ce hare-haren kan Iran na iya haifar da irin wannan tasiri a fannin tattalin arziki ga miliyoyin mutane, kuma gwamnatinsa na duba matakan da za ta ɗauka domin rage illa.
Kazalika, Sanchez ya buƙaci a bi hanyar tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙin Iran, yana mai cewa ana iya adawa da wata gwamnati ba tare da goyon bayan tsoma bakin soja ba.
Trump ya soki Birtaniya
Trump ya kuma nuna rashin jin daɗinsa da matakin Birtaniya na ƙin bai wa Amurka da Isra’ila goyon bayan da suke buƙata a yaƙin da suke gwabzawa da Iran.
Trump ya soki Firaminista Keir Starmer, yana cewa ba shi da jajircewar tsohon jagoran Birtaniya, Winston Churchill.
Ko da yake Starmer ya amince jiragen yaƙin Amurka su yi amfani da wasu sansanonin Birtaniya don “ƙayyadadden aikin kariya,” amma bai ba da izinin amfani da sansanonin Cyprus ba.
Trump ya kuma sake sukar shirin mayar da Tsibirin Chagos ga Mauritius tare da yarjejeniyar hayar sansanin Diego Garcia, yana mai cewa Birtaniya ba ta ba da haɗin kai yadda ya kamata ba.
Rikicin ya sake bayyana saɓanin da ke tsakanin Amurka da wasu ƙawayenta kan yadda za a tafiyar da yaƙin Iran da kuma batun ayyukan tsaro a NATO.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link