An Ɗage Jana’izar Ayatollah Ali Khamenei Saboda Yawan Jama’a

[ad_1]

Kafafen yaɗa labaran Iran sun sanar da cewa an ɗage taron jana’izar jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka shirya yi a daren yau Laraba a birnin Tehran, a Masallacin Ruhollah Khomeini.

An ce an ɗage taron ne saboda fargabar yawan jama’a da za su halarta, inda ake hasashen miliyoyin mutane za su taru.

  • Yau Za A Fara Jana’izar Ayatollah Khamenei A Tehran
  • Wang Yi Ya Tattauna Da Ministan Wajen Isra’ila Ta Wayar Tarho

Haka kuma ana buƙatar yin tsari na musamman domin tabbatar da an gudanar da taron cikin tsari da lumana.

Rahotanni sun ce an kashe jagoran ne a wani harin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila a ranar Asabar.

Harin ya haddasa tashin hankali da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Har yanzu ba a sanar da sabuwar ranar da za a yi jana’izar ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *