Ministocin Tsaro sun kai ziyara Maiduguri don tantance yanayin tsaro

[ad_1]



Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (Ritaya), tare da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, sun isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin duba halin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

An tarbe su a sansanin sojin sama da ke Maiduguri, inda Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation HADIN KAI, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya jagoranci tarbar su tare da wasu manyan hafsoshin soji.

Wannan shi ne karo na farko da Janar Musa ya kai ziyara a Borno tun bayan naɗa shi Ministan Tsaro a watan Disamba, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ziyara na da nasaba da sake farfaɗowar ’yan ta’adddan Boko Haram da ISWAP a yankin, lamarin da ya sa sojojisuka ƙara kaimi wajen fatattakar su.

Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya sojoji sun hana yunƙurin sace matafiya 150 a hanyar Buratai–Kamuya da ke Biu, sannan suka kashe akalla ’yan ta’adda 38 da suka kai hari a sansanin soji na Mandaragirau.

A yayin ziyarar, ministocin sun kai gaisuwa ga Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, inda suka jajanta masa da al’ummar jihar kan hare-haren boma-boman da aka danganta da Boko Haram.

Janar Musa ya yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai jaddada cewa ba su da alaƙa da addini ko wata hujja ta gaskiya.

A cewarsa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarce su da su zo su yi ta’aziyya ga al’ummar Borno.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na ɗaukar matakan da suka dace domin kauce wa maimaituwar irin waɗannan hare-hare.

A nasa jawabin, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya tabbatar da ƙudirin gwamnati na kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin kasar.

Matawalle ya kuma yaba wa Shehun Borno bisa rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *