Sibil Difens ta kama mutum 6 kan satar ƙarfen digar jirgin ƙasa a Kano

[ad_1]



Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Kano, ta kama mutum shida da ake zargi da satar ƙarfen digar jirgin ƙasa a Ƙaramar Hukumar Kiru.

Kwamandan hukumar a jihar, Mohammed Hassan Agalama ne, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanai da kuma sa ido da jami’ai suka yi.

Agalama, ya bayyana wannan aiki a matsayin lalata tattalin arziƙi da kuma barazana ga tsaron jama’a.

Waɗanda aka kama, dukkaninsu ’yan asalin Jihar Kaduna ne, sun haɗa da Sulaiman Salisu mai shekaru 45, Musa Aliyu Harisu (22), Ishaq Alhassan (20), Isa Aminu (35), Sadiq Bala (20) da Mansur Idris (22).

Kayan da aka ƙwato sun haɗa da ƙarfen jirgin ƙasa da aka lalata, ƙusoshi 60, da kayan aiki kamar tankunan gas da bututun roba da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.

Bincike ya nuna cewa suna shirin sayar da kayan ne domin samun kuɗi.

Kwamandan ya jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci lalata kadarorin gwamnati ba, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *