An Kama Mutane Shida Da Ake Zargi Da Lalata Layin Dogo A Kano – NSCDC

[ad_1]

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), reshen Jihar Kano, ta kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen cirewa da satar abin ƙulle layin dogo ba bisa ka’ida ba a Ƙaramar Hukumar Kiru ta jihar.

Kwamandan NSCDC na jihar, Mohammed Agalama, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar a ranar Laraba.

Ya ce, “Hukumar NSCDC reshen Jihar Kano na sanar da al’umma cewa ta kama wasu mutane shida da ake zargi da lalata tare da satar katakon layin dogo a Ƙaramar Hukumar Kiru ta Jihar Kano.”

A cewarsa, jami’an hukumar masu lura da tsaro sun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da gudanar da aikin sa ido na musamman.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *