Mutane 7 Sun Mutu, 4 Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Mota A Yobe
[ad_1]
Mutane bakwai sun rasa rayukansu yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a yankin Badejo na Jihar Yobe. Hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Juma’a, inda ya rutsa da motar bas kirar Sharon dake ɗauke da fasinjoji daga Lawanti a Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe zuwa Maiduguri, Jihar Borno.
Rundunar Ƴansandan Jihar Yobe ta bayyana cewa tayar baya ta motar ta fashe ne a lokacin da take tafiya, lamarin da ya sa direban ya kasa shawo kan motar, ta fita daga hanya tare da fadawa cikin daji. Direban da wasu fasinjoji huɗu sun mutu nan take, yayin da wasu shida suka samu munanan raunuka.
- Bam Ya Hallaka ‘Yan Sa-kai Biyu A Yobe
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe
Jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa sun garzaya wurin domin ceto waɗanda suka jikkata tare da kai su Asibitin Kwararru na Jihar da ke Potiskum. Sai dai rahoton ya nuna cewa biyu daga cikin waɗanda aka kai asibitin sun rasu yayin da ake ƙoƙarin ba su kulawa.
Kwamishinan Ƴansandan Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa. Ya kuma gargaɗi direbobi da su kiyaye dokokin hanya, su guji gudu fiye da kima, tare da tabbatar da duba lafiyar motocinsu, musamman tayoyi, domin kauce wa aukuwar irin wadannan hatsarori.
[ad_2]
Source link