Gwamnonin Arewa Sun Yi Tir Da Tashin Bama-bamai A Maiduguri

[ad_1]

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allawadai da fashewar jerin bama-bamai masu muni da suka girgiza Maiduguri a ranar Litinin, inda ya bayyana harin a matsayin na rashin imani, na ta’addanci a kan fararen hula.

Rahotanni sun nuna cewa tashin jerin bama-bamai wadanda wasu ‘yan kunar bakin wake suka aiwatar sun tashi ne a lokaci guda da yammacin ranar Litinin a kasuwar Maiduguri Monday Market, kofar shiga asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da kuma Post- Office flyober dukka a Maiduguri babbar birnin jihar Borno.

  • Shettima Ya Ziyarci Waɗanda Harin Bam Ya Shafa A Maiduguri
  • Ana Neman Hankada Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Mummunan Rami In Ji Wakilin Kasar Sin

‘Yansanda sun ce mutane 23 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu sama da 100 suka jikkata.

A cikin sanarwar da ya fitar a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matukar jimami da alhininsa kan wannan mummunan hare-haren, tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Borno, musamman iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu.

Inuwa wanda kuma shi ne gwamnan jihar Gombe ya ce, “Wannan mummunan aika-aikar na tashin hankali ba wai kawai abin kyama ba ne, wani yunkuri ne na zalunci da nufin haifar da tsoro da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar da ake kokarin dawo da shi a yankin Arewa maso Gabas.”

Sanarwar da Isma’ila Uba Misilli, Darakta-Janar na harkokin yada labarai na gidan jihar gwamnatin Gombe ya sanya wa hannu, Gwamna Inuwa ya ce, dole ne a yi Allah-wadai da hare-haren.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ya jajanta wa wadanda ke kwance a asibiti a halin yanzu domin samun kulawar likitoci sakamakon raunuka da suka samu a hare-haren, tare da yi musu addu’ar samun sauki cikin gaggawa.

Kazalika, ya kuma yaba wa jami’an agajin gaggawa da hukumomin tsaro kan yadda suka gaggauta daukar mataki wajen shawo kan halin da aka shiga bayan fashe-fashen.

Ya sake jaddada kudurin gwamnonin Arewa na ci gaba da aiki kafada-kafada da Gwamnatin Tarayya da kuma hukumomin tsaro domin yakar dukkan nau’o’in ta’addanci da ayyukan laifi da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar arewa maso gabas.

Inuwa ya budaci mazauna al’ummar Maiduguri da sauran yankunan da suke shiyyar da su kwantar da hankulansu, su kasance masu ci gaba da bin doka da oda, tare da bada cikakken hadin kai da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen binciken da ake yi da kuma taimaka musu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso domin dakile ayyukan ta’addanci.

“A halin yanzu fiye da kowane lokaci, wajibi ne mu tsaya tsayin daka tare domin yakar makiyan zaman lafiya. Ba za mu yi kasa a guiwa kan yunkurinmu na dawo da zaman lafiya a shiryar arewa maso gabas ba, tare za mu kawo karshen wannan matsalar tsaron,” ya jaddada.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hare-haren, tare da kira ga hukumomin tsaron da su kara zage damtse domin ganin an kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aika-aikar kuma a hukunta su cikin gaggawa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *