Mutum Biyu Sun Rasu Yayin Rikici Tsakanin Jami’an Tsaro Da Matasa A Katsina

[ad_1]

Mutum biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakanin jami’an tsaro da wasu matasa a unguwar Sabuwar Unguwa da ke birnin Katsina. Lamarin ya faru ne lokacin da ƴansanda suka kai sumame wata maɓoya a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun cafke wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi mai suna Uzairu, wanda aka fi sani da Kuda, tare da kama shi da miyagun ƙwayoyi da makami mai haɗari. Sai dai an ce wanda ake zargin ya bijire wa kama shi, yayin da abokan hulɗarsa suka kai wa jami’an hari, inda suka lalata mota tare da jikkata wasu jami’an tsaro.

  • Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wanda Aka Sace A Kan Iyakar Kano da Katsina
  • Gwamna Radda Ya Dora Harsashin Gina Ma’aikatar Sarrafa Rogo A Katsina

A yayin rikicin, an harbi Kuda, daga bisani ya rasu a asibiti. Jana’izarsa da aka gudanar a ranar Asabar ta rikiɗe zuwa tashin hankali, inda wasu da ake zargi ƴan daba ne suka ƙona ofishin NSCDC tare da yunƙurin ƙona ofishin ƴansanda, lamarin da ya sa aka tura ƙarin jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.

Rundunar ƴansandan Jihar Katsina ta ce an ƙaddamar da bincike mai zurfi kan lamarin, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu. Kakakin rundunar, DSP Abubakar Aliyu Sadiq, ya ce Kwamishinan ƴansanda ya umarci cikakken bincike don gano gaskiyar abin da ya faru, yana mai roƙon jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu tare da ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *