An Hallaka Mutum Biyu, An Sace Huɗu A Gombe

[ad_1]

Wasu da ba a tantance su ko su waye ba sun hallaka mutum biyu, Yusuf Daddy da ƴar uwarsa Faiza, tare da sace wasu mutane huɗu a garin Pindiga da ke Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe. Lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Asabar, inda maharan suka kai hari cikin gidajen jama’a kafin su tsere.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allah-wadai da kisan gillar, yana mai bayyana harin a matsayin abin tausayi, da rashin imani da kuma abin da ba za a amince da shi ba. Ya ce kashe fararen hula tare da sace mata da yara babban laifi ne da ya saɓa wa ɗabi’ar dan Adam, tare da barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

  • Yadda Wani Matashi Ya Kashe Abokin Aikinsa A Fadar Gwamnatin Gombe
  • Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

A wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamna, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun fara bincike mai zurfi, tare da umarnin a yi amfani da dukkan hanyoyi wajen gano masu hannu a lamarin da kuma ceto waɗanda aka sace cikin gaggawa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada cewa Jihar Gombe ba za ta zama mafakar masu aikata laifuka ba, yana mai kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da ba hukumomin tsaro haɗin kai. Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Pindiga, tare da addu’ar Allah ya ji ƙan waɗanda aka kashe, ya kuma dawo da waɗanda aka sace lafiya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *