Manyan Badaƙala 5 a Najeriya a 2025
[ad_1]
An samu wasu manyan zarge-zargen almundahana da aikata laifukan kuɗi a kan wasu fitattun mutane a shekarar 2025 da muke bankwana da ita.
Ga jeri wasu fitattu daga ciki.
– Abubakar Malami
Daga cikin su akwai tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari, wato Abubakar Malami, SAN, tare da ɗansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da wata makusanciyarsa, Hajiya Bashir Asabe.
Ana zargin Malami da sauran mutanen ne da aikata laifukan safarar kuɗi da kuma mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda darajarsu ta kai naira biliyan 8.7.
A karshe kotu ta ba da umarnin tsare suna gidan yari kafin daga bisani alƙali ya ba da belinsu.
– Timipre Sylva
Haka kuma, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ayyana tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ministan Man Fetur, Timipre Sylva, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a watan Nuwamban 2025, bisa zargin damfarar dalar Amurka miliyan 14.85.
Zargin ya danganci kuɗaɗen da ake alaƙantawa da Hukumar Kula da Ci gaban Abun Cikin Gida ta Najeriya (NCDMB) da kuma kamfanin matatar mai na Atlantic International Refinery.
Ana tuhumar Sylva da haɗa baki da kuma karkatar da kuɗi, inda Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar da sammacin kama shi.
Zargin badaƙalar ya kunno kai ne alhali Sylva tana ƙasar waje.
– Chris Ngige
A cikin shekarar ce Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta tura tsohon Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, zuwa gidan yari kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.2.
An tsare shi a Gidan Gyaran Hali na Kuje, bisa tuhume-tuhumen da EFCC ta shigar a kansa.
-Mele Kyari
A cikin shekarar kuma, jami’an EFCC suka yi wa tsohon Shugaban Rukunin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, tambayoyi kan zargin aikata ba daidai ba a harkar kuɗi a lokacin da yake kan mukaminsa.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta gayyace shi ne domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen da ake yi masa.
– Hankalin Nnaji
A watan Oktoba, Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga muƙaminsa bayan ɓullar zargin cewa ya yi amfani da takardun shaidar karatu na bogi a lokacin tantance shi domin nada shi minista.
Da farko, Nnaji ya musanta zargin, inda ya jaddada cewa ya kammala karatunsa a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN), da digiri a fannin Microbiology/Biochemistry.
Sanar da murabus ɗinsa ta fito ne daga fadar shugaban kasa, abin da ake ganin an yi ne domin kare gwamnati daga ƙara jin kunya da badaƙala.
– Faruk Ahmad
A watan Disamba, wanda ya kafa Matatar Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya fito fili ya zargi Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Albarkatun Mai na Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, da aikata ta’addanci ga tattalin arziki.
Ɗangote ya miƙa takardar koke ga Hukumar ICPC, inda ya buƙaci a binciki abin da ya bayyana a matsayin dukiya mai cike da shakku da Farouk Ahmed ya mallaka.
Daga cikin zarge-zargen akwai iƙirarin cewa hukumar ta biyan kusan naira miliyan 5 domin karatun sakandaren ’ya’yan Farouk Ahmed guda hudu a kasar Switzerland.
Ɗangote ya tambayi asalin dukiyar babban jami’in da kuma yadda zai iya ɗaukar nauyin irin wannan kuɗi domin ilimin ’ya’yansa.
Zargin ya ƙara tsananta ne bayan Dangote ya rubuta wasika a hukumance ga ICPC, yana neman a gudanar da cikakken bincike.
Daga bisani, fadar shugaban ƙasa ta sanar da murabus din Farouk Ahmed daga mukaminsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link