Ya Kashe Dan Uwansa Saboda Kin Ba Da Gudunmawar Naira 1,000
Taron iyali ya rikide zuwa mummunan lamari a Jihar Delta, bayan wani mutum mai shekaru 47 ya kashe dan uwansa na farko, bisa zargin rikici mai zafi kan dowo masa da Naira 1,000.
Lamarin, wanda ya faru a ranar 12 ga Disamba, 2025, a Karamar Hukumar Ughelli South, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Delta, SP Edafe Bright, ne ya tabbatar da haka a wani bidiyo da aka wallafa a shafin D ranar Litinin.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Ta Farko Game Da Tattalin Arziki Mai Alaka Da Yanayin Duniyarmu
- An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce
A cewar Edafe, iyalin sun dawo ne daga jana’izar wani daga cikin danginsu, sannan suka zauna domin yin taron iyali.
Sai dai yanayin ya lalace lokacin da aka samu sabani kan dawo gudummawar Naira 1,000.
Edafe ya ce: “Wannan matashin yana ta ja da rigima, yana tayar da hayaniya yana cewa dole sai an mayar masa da 1,000 dinsa.”
Ya ci gaba da cewa, “A yayin jan-rigimar, ya fara fada. A wani lokaci, a cewarsa, yayin da yake kokarin kubuta daga fadan, sai ya yi amfani da hannunsa ya bugi daya daga cikin ‘yan uwansa, wanda daga bisani ya rasu.
“Yanzu ga shi, gardamar Naira 1,000 ta kai ga mutuwar wani dan uwa. An rika gargadinsa har ma da wannan mutumin da daga karshe ya rasu.
“Ruhin da ya shiga jikinsa, a cewarsa, bai bar shi ya saurari ‘yan uwansa ba. Mutumin da ya mutu yana da shekaru 42, ya mutu kawai saboda Naira 1,000.”
Wanda ake zargin, mai suna Ezekiel, mai shekaru 47, ya nuna nadama yayin da yake magana, tare da ikirarin cewa mutuwar hatsari ce.
Ya amince cewa ‘yan uwa da dama, ciki har da mamacin, sun roke shi da ya kwantar da hankalinsa. “Kuskure ne. Ban ma san lokacin da na buge shi ba,” in ji shi.
Ezekiel ya bayyana cewa kudin Naira 1,000 da ake magana a kai gudummawa ce da aka bayar domin bukukuwan jana’iza, wadda bisa al’ada ake mayar wa mai ita bayan an kammala jana’izar.
“Bayan an kammala komai, sukan raba kudin. Haka ne muke mayar wa mai kudin nasa,” in ji shi.
Edafe ya yi amfani da faruwar wannan mummunan lamari wajen kira ga jama’a da su kame zuciya, ko da a lokacin kananan abubuwan da ke tayar da hankali.
“Nawa kawai shi ne in yi magana da masu sauraronmu su fahimci muhimmancin sarrafa fushi. Dole ne ku kwantar da hankali. Duk wani nau’in fada na iya kai wa ga mutuwa. Zai iya zama kisan kai ba da gangan ba. Zai iya zama kisan kai. Don Allah, magana kadan ta isa ga mai hikima. Rigakafi ya fi magani,” Edafe ya kammala.
Jaridar PUNCH ta ruwaito a shekarar 2023 cewa wani mutum mai suna Ibrahim Dauda ya kashe dan uwansa, Tunde, bisa zargin rikici kan Naira 1,000, a gidansu da ke yankin Igando na Jihar Lagos.
A baya-bayan nan, a watan Satumba, rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta kama wani mai suna Okwuchukwu Ezimuo bisa zargin soka wa dan uwansa wuka har ya mutu, sakamakon rikicin filin iyali a Karamar Hukumar Idemili South ta jihar.