Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

[ad_1]

Dai dai lokacin da ake ci gaba da tababa tsakanin Amurka da Iran kan ikirarin Donald Trump da ke cewa ya yi magana da mahukuntan kasar ta gabas ta tsakiya kuma a shirye suke a fara tattaunawar sulhu don kawo karshen rikicinsu, Tehran ta nanata cewa kalaman na Trump ba komai ba ne face zunzurutun karya da kokarin karkatar da hankalin duniya.

Gwamnatin Tehran ta musanta cewa an yi tattaunawa tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kakakin majalisar kasar Mohammed Bagher Ghalibaf, wanda tun farko shi ne Amurkan ta yi ikirarin cewa ya shiga tsakani, matakin da gwamnatin ta Iran ke cewa ba komai ba ne face yunkurin Washington na haddasa yamutsi a kasuwar makamashi.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamfara
  • Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)

Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya tattaunawa da wani kusa a gwamnatin Iran kuma kasar a shirye ta ke ta hau teburin sulhu don kawo karshen wannan yaki, yana mai cewa kasar ta gabas ta tsakiya ta wahala matuka.

Yayinda aka shiga rana ta 25 da faro wannan yaki da tuni ya dagula lamurra a kusan dukkanin sassan duniya musamman gabas ta tsakiya, ana ci gaba da kaiwa juna hare-hare tsakanin Iran da Isra’ila inda rundunar juyin-juya hali ta IRGC ke cewa ta tare tarin jirage marasa matuka da suka keta sararin samaniyar Tehran.

A gefe guda an jiyo karar kuwwar ankararwa a Acre da Kryot da ke Haifa bayan makamai masu linzami da Hezbollah ta harba daga Lebanon, wanda ke matsayin kari kan luguden makaman rokar da Iran ta yi a birnin Tel Abib duk a safiyar ta yau Talata.

Isra’ila ta ce ta kai hari cibiyoyin tattara bayanan sirri na dakarun juyin juya halin Iran tare da ikirarin lalata na’urorin da ke aikin a sashen.

Haka zalika Isra’ila ta ce ta lalace tarin rumbunan adana makaman Iran.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *